Tsofaffin sojoji sun yi zanga-zanga a Abuja

Sojoji a bakin aiki a Najeriya
Image caption Sojoji a bakin aiki a Najeriya

Daruruwan sojojin da suka yi ritaya ne a Najeriya, suka yi zanga-zangar lumana a babban birnin kasar Abuja, bisa bukatun da suka shafi hakkokinsu.

'Yan fanshon sun yi tattaki daga dandalin Eagle dake tsakiyar birnin, zuwa majalisar dokokin kasar domin mika korafinsu.

Tsofaffin sojojin dai na bukatar a biya su kashi 53 cikin dari, na kudaden rarar fanshonsu tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu.

Tare da aiwatar da karin kudi kan fanshon da suke karba duk wata.

'Yan fanshon sun kuma nemi gwamnatin Najeriya ta dinga lura da lafiyarsu kyauta, kansacewar kashi 90 cikin dari na mambobinsu sun haura shekaru 60.

A Najeriyar dai an sha samun tsofaffin sojojin dake mutuwa a kan layin karbar hakkokinsu.

Hakan na faruwa ne duk da ikirarin hukumomi na kyautata harkar fansho a kasar.