Bam ya hallaka mai tsaron shugaban Pakistan

Bilal Shaikh

Bam ya tashi a Karachi birni mafi girma a kasar Pakistan, inda ya hallaka babban mai tsaron lafiyar Shugaban kasar, Bilal Shaikh da kuma wasu mutane biyu. Wani babban jami'in 'yan sanda ya ce bam din ya yi kaca-kaca da motar da Mista Shaikh ke ciki, motar da harsashi baya huda ta. Binciken farko da 'yan sanda suka yi ya nuna cewa an yi wa Bilal Shaikh din kwanton bauna ne , aka bude masa wuta bayan fitowa daga mota a wani wuri mai cike da jama'a .

A baya dai Bilal Sheikh ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka yi kokarin kashe shi a mahaifar tasa, Karachi , a bara. Tuni Shugaba Asif Ali Zardari ya yi Allawadai da harin.