Ana mahawara kan kundin tsarin mulki

Image caption An fara mahawara a kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya

A Najeriya, majalisar dattawan kasar ta fara muhawara a kan ra'ayoyin da kwamitin majalisar ya tantance game da yunkurin da suke yi na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran-fuska.

An dai shiga wani mataki da ake baiwa kowane dan majalisar damar fadar matsayinsa a kan ra'ayoyin.

Mafi yawansu na sukar batun sauya wa'adin mulkin shugaban kasa da gwamnoni zuwa wa'adi daya tilo mai shekara shida.

Ali Ndume sanata daga yankin kudancin Borno, ya shaidawa BBC cewa shi ma ba shi da ra'ayin wa'adin mulkin shugaban kasa da gwamnoni zuwa wa'adi daya tilo mai shekara shida.

Karin bayani