Kotu ta wanke Manjo Hamza Al-Mustapha

Image caption Manjo Hamza Al-Mustapha

Kotun Daukaka Kara ta Najeriya shiyyar Legas ta soke tuhumar da ake yi wa Manjo Hamza Al-Mustapha, sannan ta wanke shi daga duk wani laifi.

Shekaru 14 ke nan tsohon dogarin na Marigayi Janar Sani Abacha ya kwashe a gidan yari, sai dai kuma kotun ta bayyana tsare shi da cewa akwai siyasa a ciki.

Da hakan dai Kotun ta Daukaka Kara ta warware hukuncin da Babbar Kotun Jihar Legas ta yanke a watan Janairun bara, inda ta same shi da hannu a kisan Kudirat Abiola, matar Cif MKO Abiola--mutumin da aka yi amanna shi ne ya lashe zaben 12 ga watan Yunin shekara ta 1993--ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

Karin bayani