Amurka na shirin tura jiragen yaki Masar

Jirgin yakin Amurka
Image caption Jirgin yakin Amurka

Amurka ta ce tana da aniyar tura jiragen yaki hudu kasar Masar, kamar yadda aka tsara nan da makwanni masu zuwa, duk kuwa da rikicin siyasar da kasar ke ciki.

Fadar White House ta ce tana duba hukuncin da sojojin Masar suka dauka, na hambarar da shugaba Morsi daga mulkin kasar.

Ya kamata dai Amurka ta dakatar da agajin da take ba wa kasar Masar, matsawar ta tabbatar abin da ya faru a kasar juyin mulki ne.

Sai dai shugaba Obama na yin taka-tsan-tsa wajen furta hakan.

A bangare daya kuma, 'yan sandan Masar na ci gaba da neman shugaban jam'iyyar 'yan uwa Musulmi, ta hambararren Shugaba Morsi da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar.