Benaye sun rufta kan mutane a Najeriya

Anyi asarar rayukan mutane da dama a Najeriya bayan da wasu benaye suka rufta a biranen Lagos da Kaduna.

Akalla gawawwakin mutane 11 ne aka zakulo daga cikin buragujan wani bene mai hawa ukku da ya rufta a Lagos.

A Kaduna kuma ana can ana kokarin ceto mutanen da ba a san adadinsu ba a wani gini hawa ukku da ya ruguje a titin Hadejia dake cikin birnin.

Tun kimanin karfe biyu na rana ne dai wannan gini, wanda mazauna unguwar suka ce tsoho ne, ya rufta akan dukkan wadanda ke cikinsa a lokacin.

Rashin kayan aikin zakulo jama'a dai ya sanya sai da aka shafe sa'o'i ba tare da fara ceto wadanda ginin ya danne ba.

Mutane biyu ne kawai jama'a suka yi nasarar zakulowa kafin zuwan jami'an tsaro.

A Lagos din kuwa benen mai hawa ukku dake unguwar Ebute Metta ya rufta ne yau akan mutane da dama.

Ma'aikatan agajin gaggawa sun zakulo gawarwaki 11 da kuma wasu mutane 14 da suka samu munanan raunuka.

Har zuwa lokacin aiko da rahoton nan dai hukumomin kai agajin gaggawa na ci gaba da zakulo mutane a wajen.

Karin bayani