China ta zargi Glaxo Smithkline da zamba

Daya daga cikin magungunan Glaxo
Image caption Daya daga cikin magungunan Glaxo

Hukumomin China sun ce suna tuhumar wasu manyan shugabanin kamfanin harhada magunguna mafi girma na Birtaniya GlaxoSmith Kline game da zargin cin hanci da kuma kaucewa biyan haraji.

Ma'aikatar tsaron al'umma ta China ta ce shugabannin sun bada dumbin cin hanci ga jami'ai da kungiyoyin kiwon lafiya da asibitoci da kuma likitoci domin habaka sayar da magungunansu.

Hukumomin sun ce mutanen da ake zargin wadanda ba a bayyana sunayensu ba sun amsa aikata laifin. Kamfanin na GlaxoSmith Kline ya ce zai bada hadin kai ga hukumomin sai dai ya ce bai ga wata shaidar cin hanci kokarbar rashawa daga ma'aikatan nasa dake China ba.