China za ta ba Najeriya bashin $1.1b

Kudin Yuan na kasar China
Image caption Kudin Yuan na kasar China

Kasar Sin ta amince ta baiwa Najeriya bashin dalar Amurka sama da biliyan daya ba tare da dora kudin ruwa mai yawa ba, domin samar da ababen more rayuwa.

Da yammacin ranar Laraba ne shugabannin kasashen biyu, Goodluck Jonathan da Xi Jinping suka jagoranci rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Najeriyar za ta yi amfani da kudin ne wajen gina filayen jiragen sama hudu da gina tituna da kuma layin dogo.

Za a gina sababbin filayen jiragen saman a biiranen Kano da Lagos da Abuja da kuma Patakwal.

Ministan tsare-tsare na kasa Dr. Shamsudden Usman, wanda ke cikin tawagar Najeriya, ya ce kasar ta Sin ta kuma baiwa Najeriya kyautar kudin China Yuan miliyan 80 domin tafi da tattalin arzikinta.

Inda ya kara da cewa kamfanin makamashi na China power ya nuna sha'awar zuba jari a fannin wutan lantarki na Najeriya.

Dr. Goodluck Jonathan na yin wata ziyara ta kwanaki hudu ne a China.

Kasar Sin dai na zuba jari sosai a nahiyar Afrika, kuma ta dogara da ita domin samun man fetur da sauran ma'adanai.

Kuma Najeriya na daya daga cikin manyan kasashen duniya dake samar da danyen man fetur.