Jami'an tsaro sun kai samame a Sokoto

Wani sojan Najeriya
Image caption Rundunar sojin Najeriya na cigaba da fuskantar kalubalen tsaro a kasar

Jami'an tsaro sun shafe kusan sa'oi bakwai suna musayar wuta da wadansu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne a unguwar Gidan-Sanda dake birnin Sokoto a arewacin Najeriya.

A wani taron manema labarai da suka yi bayan an gama musayar wutar, sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun samu bindigogi 20 da albarusai a gidan mutanen dake karamar hukumar Wamakko a jihar ta Sokoto.

Sun kara da cewa sun kashe mutum guda sun kuma wani da matansu da kuma yaransu.

Haka kuma sun rushe gidan da mutanen ke ciki.

Tun da misalin karfe biyun daren ranar Laraba ne dai aka fara jin harbe-harbe har zuwa karfe tara na safiyar ranar Alhamis.

Samamen sojin dai ya biyo bayan wadansu bayanan sirri ne da jam'an suka ce sun samu kuma sun shafe kwanaki suna bincike a kai.

Ko da yake sojojin ba su ce komai game da ko an samu jikkata a bangerensu ba, wani dan jarida ya shaida wa BBC cewa ya ga wani jami'in rundunar tsaro ta farin kaya, wato SSS, ya samu rauni.

Jihar Sokoto dai jiha ce dake cikin jihohin dake da kwanciyar hankali a arewacin Najeriya, duk da hare-hare da kashe-kashen dake faruwa a yankin.