'Yan gudun hijirar Congo sun tsallaka Uganda

Image caption 'Yan gudun hijira na neman mafaka

Dubban 'yan gudun hijira daga jamhuriyar Dimokradiyyar Congo suna ta kaura zuwa makwabciya kasar Uganda domin gujewa kazamin fada.

Arangama ta barke ne a garin Kamango dake kan iyaka tsakanin sojoji Congo da yan kungiyar tawaye ta Allied Democratic Force (ADF) wadda ke fafutukar hambarar da gwamnatin Uganda da kuma ta mayar da sansanoninta gabashin Dimokradiyar Congo.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira akalla dubu goma sha takwas ne suka tsallaka cikin Uganda domin neman mafaka tun bayan harin da aka kai garin Kamango a ranar Alhamis.

Karin bayani