An halarta zubar da ciki a Ireland

Image caption An halarta zubar da ciki a Ireland

A karon farko 'yan majalisar wakilai ta Ireland sun yanke hukuncin halasta zubar da ciki a wasu kayyadaddun lokuta.

Kudirin dokar ya samu wucewa da gagarumin rinjaye,bayan wata zazzafar mahawara tsakanin mutanen kasar, wanda mafi yawan su mabiya darikar Roman Katolica ne.

An bada damar zubar da cikin ne idan har rayuwar uwar na cikin hadari.

Kakakin majalisar, Sean Barrett shi ya sanar da sakamakon.

An dai sauya dokar ne a lokacin da wata mata za ta yi bari,amma likitoci ba su da damar zubar da cikin, abin da ya yi sandiyar mutuwarta.

Karin bayani