China ta soke kafa ma'aikatar nukiliya

Hukumomi a birnin Jiangmen a kudancin China sun ce za su soke shirin gina wata ma'aikatar nukiliya da suka shirya yi bayan zanga zangar da wasu daruruwan jama'a suka yi don nuna adawa da shirin.

Masu zanga zangar sun ce hukumomin suna gaggawar shirin gina ma'aikatar ce ba tare da sun ji ra'ayoyin jama'a ba.

An shirya sake gudanar da zanga zangar a gobe Lahadi ma.

Kafofin yada labarai sun soki lamirin mahukuntan birnin da yin gaba gadi domin gudanar da aikin ba tare da binciken illar da zai yi ga muhalli ba.

Wani jami'in gwamnatin Chinan ya ce gwamnati na sauraren bukatun jama'a, saboda haka ne ta soke shirin.

Jama'ar yankin sun ta shewa yayinda suka ji sanarwar cewa an soke shirin.

Da yawansu sun yi nuni da cewa shawarar da gwamnatin ta yanke na skoe shirin ta yi kyau sosai.

Sai dai sun yi nuni da cewa irin adawar da suka nuna ce ta tilasta wa gwamnatin daukar wannan mataki.

Karin bayani