Hukumomin Masar na binciken Morsi

A Masar ofishin babban mai gabatar da kara na gwamnati ya bada sanarwar cewa yana binciken wasu laifuka da ake zargin hambararren shugaban kasar, Mohammed Morsi, da wasu shugabannin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aikatawa.

Zarge zargen sun hada da leken asiri da tunzura kisan masu zanga zanga da kai hari akan barikokin soji da kuma lalata tattalin arziki.

Kasashen Amurka da Jamus sun bukaci a saki Mohammed Morsi a kuma daina kama shugabannin kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi.

A halin da ake ciki kuma shugaban majalisar dattijai ta kasar wadda aka sauke, Ahmed Fahmy, ya soki lamirin kawar da shugaba Morsi daga karagar mulki.

Ya ce: "Muna jaddada cewa majalisar dattijai ba ta yarda da duk wani abu da ya shafi wannan juyin mulki ba.

"Mun kuma yi amanna duk wani abu da ya fito daga juyin mulkin haramtacce ne, ya saba da kundin doka da kuma ka'idojin kasa da kasa".

Karin bayani