Harin bom ya kashe mutane 20 a Iraqi

Harin bom a Iraqi
Image caption Harin bom a Iraqi

Mutane sama da 20 sun hallaka, da dama sun jikkata , a hare-haren bama-baman da aka kai kan masallatan 'yan Sunni 2, dake Bagadaza babban birnin kasar.

An dai kai harin kan mutanen ne jim kadan bayan sun gama buda-baki.

An kuma kashe wasu mutanen bakwai a wasu jerin hare-haren da aka kai wasu sassa na kasar ta Iraqi.

A yammacin kasar, 'yan sanda sun yi arangama da wasu masu dauke da bindigogi da ba a tantance ko su wane ne ba, wadanda aka ce sun tsallako kan iyaka ne daga kasar Syria.