Shugaban Sudan ya isa Najeriya

Shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, ya isa Najeriya inda ya sami kyakyawar tarba da faretin ban girma, duk da kiran da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi na a kama shi bisa tuhumar laifukan yaki.

Shugaba al-Bashir zai halarci taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka (wato AU) a birnin Abuja akan cutattukan AIDS (ko SIDA) da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro.

Najeriya dai mamba ce a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuka (wato ICC) wadda ta tuhumi al-Bashir da laifukan yaki da keta hakkin bil'adama da kuma kisan kare dangi a Darfur.

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama a Najeriya mai suna 'Nigeria Coalition for the ICC' ta yi barazanar zuwa kotu domin tabbatar da ganin Najeriya ta cika kudirinta ga kotun ta ICC ta kama al-Bashir.

Kungiyar ta yi alwashin matsa wa gwamnatin Najeriyar lamba wajen ganin ta cafke Shugaba al-Bashir.

Wani tsohon shugaban kwamitin lura da harkokin kasashen waje na majalisar wakilai ta tarayyar Najeriyar, Dr Usman Bugaje, wanda ya dade ya na bin diddikin harkokin kasar ta Sudan, yace gangamin da ake yi na neman a kama shugaban na Sudan ya yi daidai.

Yace irin barnar da aka yi a yankin Darfur na bukatar a gurfanar da duk wanda ake zargin tabka ta a gaban kotu.

Sai dai ya ce da wuya gwamnatin Najeriyar ta kama Shugaba al-Bashir domin shugabanninta ba za su so abinda ya faru akansa ba ya faru a garesu.

Karin bayani