An bude taron Kungiyar Tarayyar Afrika

Taron kungiyar tarayya Turai
Image caption Taron kungiyar tarayya Turai

An bude taron Kungiyar Tarayyar Afrika AU a Abuja dake Najeriya, domin nazarin cututtukan AIDs ko SIDA da tarin fuka da zazzabin cizon sauro.

Shugabannin kasashen Afrikan za su kwashe kwanaki biyu suna yin nazari, kan kokarin da nahiyar ta yi wajen magance cututtukan guda uku.

Bincike dai ya nuna wadannan cuttuka na sahun gaba wajen hallaka jama'a a duniya.

El- Bashir

A bangare guda kuma, taron kungiyar tarayyar Afrikan, na neman jefa Najeriyar cikin halin tsaka-mai-wuya.

Wannan ya biyo bayan sakamakon bayanan dake nuna cewa shugaban Sudan Omar Elbashir ya isa kasar, domin halartar taron duk kuwa da cewa kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC ta ba da sammacin kama shi.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar martaba kotun, kuma tuni wasu kungiyoyin fararen-hula suka fara barazanar gurfanar da kasar gaban kuliya, domin a tilasta mata kama Omar Elbashir.

Amma masana harkokin diplomasiyya sun ce kama shugaban Sudan din, zai iya tunzura gwamnatinsa yin ramuwar gayya a kan al'ummar Najeriya dake Sudan.