Jami'an tsaro sun gano gawawwaki a Maiduguri

Jami'an tsaro a Najeriya
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

Jami'an Rundunar hadin gwiwar samar da tsaro JTF a jihar Bornon Najeriya, sun ce sun gano wani rami da aka binne tarin gawawwakin mutane da suka rube.

Mai magana da yawun rundunar ta JTF , Laftanal Kanar Sagir Musa ya ce jami'an tsaron sun kuma gano dakunan karkashin kasa na kariya daga harin bam a da 'yan kungiyar suka giggina a wata unguwa.

Ya kuma ce gawawwakin da suka gano sun hada da na 'yan kungiyar da na mutanen da 'yan kungiyar suka kashe.

Rundunar JTF ta ce ta gano wadannan wurare ne a wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, bayan hare haren da jami'an tsaron suka kai kan 'yayan kungiyar Boko Haram a makon da ya wuce .

Jami'an tsaron sun kuma ce sun samu nasarar kubutar da mata da yawa da 'yan mata da kuma yara da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kama, a wani samame da suka kai kan wata maboyar 'yayan kungiyar a Unguwar Bulabulin Nganaram.