Kungiyoyi a Najeriya na so a mika El-Bashir

Shugaba Omar Al-Bashir yayin da ya isa Abuja
Image caption Elise Keppler na kungiyar Human Rights Watch ya ce kamata ya yi a garkame shugaba ElBashir

Kungiyoyin fararen hula a Najeriya, sun yi tur da yadda gwamnatin kasar ta karbi shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir, inda suka nemi a kama shi bisa tuhumar kisan-kare-dangi.

Shugaba El-Bashir dai na halartar taron koli ne kan kiwon lafiya, wanda kungiyar Tarayyar Afrika ta shirya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Kuma an yi masa tarba ta musamman a filin jiragen sama na Abujan, a lokacin da ya isa Najeriya.

Ziyararsa a cewar wata kungiyar kare hakkin bil'adama "Cin fuska ce ga wadanda abin ya shafa."

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, na zargin shugaban da aikata kisan kare dangi, zargin da ya musanta.

A lokacin da ICC ta ba da umarnin, ita kuma kungiyar Tarayyar Afrikar ta cewa kasashen dake karkashinta kada su zartar da shi.

Inda ta zargi ICC da maido da hannun agogo baya a yunkurin samar da zaman lafiya a nahiyar.

Kana kuma ta ce ICC na farautar shugabannin Afrika ne kawai.