An kamalla taron kungiyar AU a Abuja

Image caption Wakilan kungiyar AU

Kasashen nahiyar Afirka sun amince za su dauki dawainiyar yaki da cutar AIDS ko SIDA, da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro a nahiyar.

Kasashen sun bayyana matsayinsu ne a wani kudirin da suka cimma a taron Kungiyar Tarayyar Afirka da suka kammala a Abuja.

A baya dai, nahiyar na samun sama da kashi tamanin bisa dari na kudaden da ake bukata don yakar wadannan cututtuka ne daga tallafin da manyan kasashen duniya ke ba ta.

Nigeria na daga kasashen 22 da suka fi fama da cutar tarin fuka a duniya.

Karin bayani