Hulda za ta canza tsakanin Tarayyar Turai da Isra'ila

Mrs Ashton da Mr Lieberman
Image caption Mrs Ashton da Mr Lieberman

Jami'an Israila sun soki lamirin wasu ka'idoji na kungiyar Tarayyar Turai wadanda za su haramtawa kungiyar bada tallafin kudade da kuma hadin kai ga hukumomin Isra'ila dake yankunan Falasdinawa da Isra'ilar ta mamaye.

Daga shekarar 2014 duk wani tallafin kudi na kungiyar Tarayyar Turai zuwa Israila wajibi ne a fayyace bai shafi yankunan da Isra'ilar ta mamaye ba.

Kungiyar Tarayyar Turan ta ce manufar ka'idojin ita ce rarrabewa tsakanin kasar Isra'ila da kuma yankunan da ta mamaye a gudunmawar da kungiyar ta EU za ta baiwa Israila.

Sai da ministan raya kasa na Israila Silvan Shalom ya ce haramcin ya nuna kungiyar ta Tarayyar Turai na nuna banbanci ga Israila.