Mutane bakwai sun mutu a Alkahira

Magoya bayan Morsi a lokacin arangama da sojoji
Image caption Magoya bayan Morsi a lokacin arangama da sojoji

An kashe mutane bakwai a arangamar da aka yi a daren ranar Litinin, tsakanin dakarun soji da masu goyon bayan hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda ke jifa da duwatsu tare da datse babban hanyar dake birnin Alkahira.

Arangamar ta faru ne, yayin da manzon Amurka ke ziyara a kasar, inda ya furta cewa kasar ta samu wata dama ta biyu na aiwatar da tsarin dimokradiyya.

William Burns ya gana da shugabannin rikon kwarya, amma kungiyoyin 'yan adawa ciki har da ta 'yan uwa musulmi sun yi watsi da shi.

A ranar uku ga watan Yuli ne dai sojoji suka tumbuke Mr. Morsi, abin da dama ke kallo a matsayin juyin mulki.

Sai dai soji na kare matakin da cewa sun bi abin da mutane ke so ne, bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.