Kungiyoyi sun je kotu game da El-Bashir

Shugaban kasar  Sudan al-Bashir a Najeriya
Image caption Shugaban kasar Sudan al-Bashir a Najeriya

Masu rajin kare hakkin dan adam a Najeriya na neman Kotu ta ba da damar kame Shugaban Sudan Omar al-Bashir, kuma a mika shi kotun shari'ar manyan laifukka ta duniya.

Bayan ta shigar da karar gaban Kotun Tarayya dake Abuja, gamayyar Kungiyoyin dake kare martabar Kotun duniyar ta ce, Kotun na da wajabci na aiwatar da umurnin Kotun duniyar.

Chino Obiagu shi ne jagoran kungiyoyin "Kungiyar ta Tarayyar Afrika ba ta da hujjar hana kasashen kungiyar aiwatar da umurnin Kotun duniyar."

Ko da yake alkalai na hutu yanzu a kasar, amma masu fafutukar na ganin za su iya mika wasika ga kotun ICC, domin a sanya wa Najeriya takunkumi saboda kin kama shugaban na Sudan.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin kama El-Bashir a Najeriya zai janyo dubban 'yan Najeriya mazauna Sudan su shiga wani hali a can.