"Mutane dubu biyar ke mutuwa a Siriya kowane wata" In ji Gutterres

Yakin Siriya
Image caption Yakin Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu biyar ne ke mutuwa a kowane wata a yakin dake gudana a Siriya tana mai gargadin cewa 'yan gudun hijira kimanin dubu shidda ne ke tserewa a kowace rana, matsayin da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan kisan kare dangi a Rwanda a shekarar 1994.

Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya shaidawa taron kwamitin koli cewa rikicin ya cigaba tsawon lokaci fiye da yadda kowa ya yi tsammani sannan kuma matsalolin tagaiyarar jama'a sun ta'azzara matuka.