Kotun Bangladesh ta yanke hukuncin kisa a kan wani jagoran Islama

Ahsan Muhammad
Image caption Ahsan Muhammad

Wata kotu ta musamman a Bangladesh ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan wani jagora na kungiyar 'yan kishin Islama saboda zargin aikata laifukkan yaki sama da shekaru arba'in da suka wuce, zamanin gwagwarmayar kwatar 'yanci daga Pakistan.

An samu Ahsan Muhammad Mujahid ne da aikata laifukka biyar da suka hada da satar jama'a da kuma aikata kisan kai.

Shi ne babban jami'i na biyu na jam'iyyyar Jama'at al Islami da aka yanke ma hukunci a wannan mako.

Jam'iyyar dai ta la'anci hukuncin, tana mai cewa an sanya siyasa a cikinsa.

Lauyansa ,Saifur Rahman ya ce zasu daukakak kara.