Malala ta samu wasika daga Taliban

Malala Youssoufzai
Image caption Malala na jawabi ga taron Majalissar dinkin duniya

Wani jigo a kungiyar Taliban ta Pakistan ya rubutawa yarinyar nan 'yar makaranta Malala Yousafzai wasika, a wani yunkuri na bayyana manufar kungiyar a lokacin da suka harbe ta a ka a bara.

A cikin wasikar, Adnan Rashid ya ce an kai ma ta harin ne ba wai saboda tana goyan bayan ilmin 'ya'ya mata ba, amma saboda tana gudanar da wani kamfe na kin jinin 'yan Taliban.

Ya ce ya kadu da harin da aka kaiwa Malala, kuma ya yi fatan da hakan ba ta faru ba.

Amma Adnan Rashid din ya ce ya rubuta wasikar ne a karan kansa, ba a madadin kungiyar ta Taliban ba.

Karin bayani