Iyalan Mandela na sabawa kan gawarwaki

Jikar Nelson Mandela, Ndileka Mandela
Image caption Iyalan Mandela na samun rashin jituwa kan binne gawar 'ya 'yansa

A daidai lokacin da ake shirin bikin cikar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela shekaru casa'in da biyar, daya daga cikin jikokinsa ta shaidawa BBC cewa iyalan Mista Mandela na cikin wani yanayi a dalilin mawuyacin halin da lafiyarsa ke ciki.

Ndileka Mandela ta ce tamabayoyin da ake yi dangane da ko ana taimakawa tsohon shugaban numfashi sun wuce gona da iri.

Ta kuma kara da nuna bacin ranta a kan abin da dan uwanta Mandla ya yi na sauyawa wasu daga cikin iyalan Mista Mandela kabari ciki kuwa har da mahaifinta.

Ta ce za a dauki dogon lokaci kafin a yafe masa.

Karin bayani