Majalisa ta hana kananan hukumomi 'yanci

Image caption Sanatoci sun yi fatali da cin gashin kan Kananan Hukumomi

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi fatali da shawarar baiwa kananan hukumomi hurumin cin-gashin-kansu ta yadda za su rika gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma-bakin gwamnatocin jihohi ba.

A kuri'ar da ta kada a kan shawarwarin da kwamitinta na gyaran kundin tsarin mulki ya gabatar mata, Majalisar ta yi fatali da wannan batu.

Tana mai cewa abu mafi a'ala shi ne asusun kananan hukumomin ya ci gaba da zama a karkashin kulawar gwamnatocin jihohi.

Wadansu 'yan Najeriya dai sun jima suna kiraye-kirayen a baiwa kananan hukumomi 'yancin cin-gashin-kansu, abin da ake ganin zai taimaka wajen inganta ayyukan da ake yi a matakin kananan hukumomin.

'Yan kasar da dama dai sun yi ta furta albarkacin bakinsu--wadansu suna nuna rashin goyon baya ga wannan mataki da Majalisar ta Dattawa ta dauka, wadansu kuma suna nuna goyon baya.

Karin bayani