Panama ta kama jirgin Koriya ta Arewa

Image caption Panama ta kama jirgin Koriya ta Arewa

Gwamnatin Cuba ta ce jirgin kaya na Koriya ta Arewa da aka kama a Panama na dauke ne da abin da ta kira lalatattun makaman kariya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Cuba ta ce kayan an tura su ne Koriya ta Arewa don a gyara su kafin a dawo da su Cuba.

Makaman sun hada da baturan bindigar harbo jiragen yaki kirar kasar Rasha.

Sai dai hukumomin kasar Panama sun ce jirgin kayan na soji na dauke da dubban tan-tan na sukari da aka boye a kasa-kasa.

Amurka ta ce jirgin mai suna Chong Chon Gang yana da tarihin yin fasa kwauri.

Image caption Wuraren da jirgin na Koriya ta Arewa ya ya-da-zango

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Rosemary Dicarlo ta ce idan ya tabbata cewa jirgin na dauke da makamai masu linzami, to hakan zai keta kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da dama.

Karin bayani