An jefi wasu gwamnoni a jihar Rivers

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Majalisar wakilan Najeriya ta karbe ragamar ayyukan majalisar dokokin Rivers saboda takadda tsakanin magoya baya da masu adawa da Ameachi

An jefi gwamnan jihar Rivers mai karfin fada a ji, Rotimi Ameachi da wasu takwarorinsa na arewacin Najeriya da duwatsu.

Wasu da ake tsammani magoya bayan masu adawa da shi ne suka jefe tawagar motocin gwamnonin, a lokacin da suke barin filin jirgi na Patakwal, babban birnin jihar.

Gwamnonin arewacin kasar wato na Kano da Jigawa da Niger da kuma Adamawa na ziyara a jihar ne, domin jaddada goyon baya ga Ameachi.

An dai dakatar da Mista Ameachi daga jam'iyyar PDP, saboda abin da masu sharhi suka bayyana da cewa nuna adawar da yake da shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Gwamnonin jihohi 36 na kasar dai na da matukar karfin fada a ji, saboda dumbin kasafin kudin da suke da iko da su.

Kuma ana ganin suna da tasiri wajen samun nasara a zabe.

Ana dai tsammani shugaban kasar zai sake tsayawa zabe a shekarar 2015.

Kuma masana na ganin cewa yana da muhimmancin gaske ya samu goyon bayan jihar Rivers.

Jihar ta Rivers ta jima tana fuskantar takaddamar siyasa, tsakanin masu goyon bayan Ameachi da kuma masu adawa da shi.

Lamarin da ya sa a kwanan baya aka yiwa wani dan majalisar jihar jina-jina.