Shaidu biyu sun janye daga shariar Uhuru Kenyatta

Tambarin Kotun ICC
Image caption Tambarin Kotun ICC

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ce shaidu biyu dake shirin bada bahasi a shariar shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, sun janye saboda fargabar tsaron lafiyarsu.

Ana sa ran gudanar da shariar Mr kenyatta a watan Nuwamba na shekarar da mu ke ciki a kan tuhumar aikata miyagun laifufuka.

Ana zarginsa tare da mataimakinsa Wiliam Ruto, da shirya mummunan tashin hankali bayan zaben kasar da aka yi a shekarar 2007. Sai dai dukaninsu sun musanta zargin.

Karin bayani