Najeriya za ta rage dakarunta a Mali

Najeriya na shirin janye wasu dakarunta daga Mali saboda tana bukatar sojojin a cikin gida a yakin da take yi da ta'addanci.

Shugaban kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (wato ECOWAS ko CEDEAO), Alassane Ouattara, wanda kuma shine shugaban kasar Ivory Coast, yace wata wasika ce da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya tura mashi ta nuna hakan.

Sai dai bai bayyana takamaiman yawan sojojin da Najeriyar za ta maida gida ba.

Najeriya dai na da sojoji kusan 1000 a Malin bayan da aka tura su domin yin aiki da wasu sojojin Kasashen duniya ciki harda na Faransa a kokarin da ake na fatattakar masu kaifin kishin Islama da a baya suka mamaye arewacin kasar da kuma maido da zaman lafiya a kasar.

Karin bayani