Karin mutane 2 sun mutu a fadan Masar

Image caption Fada na kara bazuwa zuwa sauran manyan biranen Masar

An kashe akalla mutane biyu a cikin wasu fadace-fadace a Masar tsakanin magoya baya da masu adawa da hambararen shugaban kasar Mohammed Morsi.

An yi fadace-fadacen ne a ranar jumu'a a birnin Mansoura da ke kusa da gabar teku.

Dubun dubatar Masarawa ne suka fantsama kan titunan Alkahira da wasu manyan biranen kasar ranar jumu'a suna kiran a maido da Morsi din bisa mulki.

Malam Morsi mai kishin addinin msulunci, shi ne shugaban Masar na farko da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya, amma sai sojan kasar suka yi masa juyin mulki a farkon watannan.