Haraji: Shugabannin G20 na taro a Rasha

Image caption Ga Sakataren kudin Burtaniya George haraji shine babban abin baiwa fifiko

Ministocin kudi daga kasashe ashirin mafi karfin tattalin arziki na G20 suna wani taro a birnin Moscow a ranakkun jumu'a da assabar.

Za su tattauna ne kan yadda za a shawo kan kaucewa biyan haraji da kuma halinda tattalin arzikin duniya yake ciki.

Manufar hakan dai ita ce hana manyan kanfunnan kasa da kasa a boye kudaden shigarda suka ci a biyawa haraji a kasashenda basu karbar haraji sosai.

Burtaniya na son wannan kungiyar, wadda ta kunshin kasashen masu tasowa ta fuskar karfin tattalin arziki ta zage dantse wajen ganin an samu musayar bayanai tsakanin hukumomin haraji na kasashen; kamar yadda kasashen da ke kan gaba a karfin tattalin arziki suka yarda suyi a wajen taron G8 a Ireland ta Arewa a watan jiya.

Karin bayani