Costa Concordia: An yanke hukunci

Image caption Jirgin Costa Concordia daya nutse

An yankewa ma'aikata biyar na kamfanin da ya mallaki jirgin ruwan nan na Costa Concordia da ya yi hadari a watan Janairun bara hukuncin dauri bisa samunsu da laifin kisa amma ba da gangan ba.

Mutane fiye da talatin ne suka suka rasu a lokacin da jirgin ya nutse a ruwa bayan da ya ci karo da dutse a gabar ruwan tsibirin Giglio na kasar Italiya.

Sai dai wakilin BBC yace akwai shakku idan daya daga cikin mutanen da suka halarci kotun da aka yankewa hukunci za su yi zaman kason.

Ana iya dakatar da kananan daurin kana a daukaka kara akan hukunci dauri mafi tsawo.

Matukin jirgin Francesco Schettino wanda ake ganin shi ya haddasa hadarin ana yi masa shari'a ne daban.