Zanga-zanga kan haramta lullubi a Faransa

Image caption Masu nikafi a Faransa

Wasu gungun daruruwan mutane sun afkawa ofishin 'yan sanda a wajen birnin Paris a wani matakin adawa da haramcin lullubi a wuraren taruwar jama'a da Faransa ta yi.

Rikicin ya faru ne bayan da wani matashi ya ci zarafin wasu 'yan sanda da ya dorawa alhakin gargadin da aka yiwa matarsa saboda yin lullubi.

'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar, an yi ta jifa da dutsu, an kuma kona wasu motoci.

Wani jami'in lardin Erard, Corbin de Mangoux ya ce akwai yiwuwar karin tashe tashen hankula.