Isra'ila za ta sako fursunonin Falasdinawa

Image caption Wani Fursunan Palasdinu

Israila ta ce tana shirin sakin wani adadi na Fursunonin Falasdinawa a wani matakin farfado da tattaunawar zaman lafiya.

Ministan hulda da kasashen duniya Yuval Steinitz yace za'a sako fursunonin ne daki-daki yana baiyana wasu daga cikinsu a matsayin jiga jigai wadanda suka shafe kusan shekaru talatin a gidan yari.

Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yace ba da jimawa ba za'a cigaba da tattaunawar zaman lafiya kai tsaye tsakanin Israila da Falasdinawa a karon farko cikin shekaru uku.

Wani wakilin BBC yace sai dai kuma bangarorin biyu har yanzu sun farraka ta fuskoki da dama kamar batun kan iyakoki da matsugunan da Israila ta mamaye da kuma matsayin birnin Kudus.

Karin bayani