2015: Ana kamun kafa wajen Cif Obasanjo

Image caption Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

A Najeriya, kokawar siyasa sai kara rincabewa take yi tsakanin bangaren shugaban kasar da wasu gwamnoni inda rahotanni ke cewa bangarorin biyun sun dukufa wajen kamun-kafar tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo.

An dai ba da labarin cewa Shugaba Jonathan ya ziyarci Chief Obasanjo a jiya Asabar, kuma yana fita wasu gwamnoni hudu daga arewacin kasar su ma suka isa gidan tsohon shugaban na Najeriya.

Gwamnonin jihohin Sokoto da Kano da Adamawa da kuma Jigawa ne suka ziyarci gidan tsohon shugaban kasar.

Dukkansu dai babu wanda ya danganta ziyarar da siyasa, amma wasu na ganin cewa ziyarar ba za ta rasa nasaba da dambarwar rikicin siyasar jihar Rivers ba, da kuma yadda lamarin zai iya shafar kasar.

Karin bayani