An sace jami'an zabe a arewacin Mali

Yankin Kidal a arewacin Mali
Image caption Yankin Kidal a arewacin Mali

Wasu 'yan bindiga sun sace jami'an zabe biyu a yankin arewacin Mali, yayinda ake shirye-shiryen zaben Shugaban kasa cikin kwanaki 8 masu zuwa.

An sace mutanen ne a garin Tessalit wanda ke dab da birnin Kidal.

Mutanen biyu, wadanda daya daga cikinsu mataimakin Magajin gari ne, suna shirin rarraba katin rajista ne na masu zabe a garin.

Akwai dai fargabar da ake yi cewar babu kwanciyar hankalin da zai ba da damar zabe a yankin na arewacin Mali.

Wannan ya biyo bayan maido da cikakken tsaro a yankin, bayan hare-haren da dakarun kasar waje a karkashin jagorancin Faransa suka dauka a farkon wannan shekarar, don fatattakar masu tayar da kayar-baya.