Ministocin Kungiyar EU za su gana

Tutar Kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Tutar Kungiyar Tarayyar Turai

Ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen Turai EU, za su gana a yau domin tattaunawa game 'yan kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon.

Za dai su tattauna ne game da kiran da ake yi na sanya bangaren soji na kungiyar Hezbollah a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Birtaniya dai ta sanya kungiyar a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a shekara ta 2008, amma tana neman amincewar dukkan kasashe mambobin kungiyar ta EU guda 28.

Idan suka amince da wannan mataki, zai zama haramun ga masu tausayawa kungiyar ta Hezbollah su aike ma ta da kudi, ko kuma ma'aikatan diplomassiyya na kasashen Turai su gana da bangaren soji na kungiyar.