Matar Yarima William ta haifi da namiji

Kate Middleton
Image caption Manema labarai na duniya sun kafa sansani a wajen asibitin na St. Mary

Matar Yarima William wato Duchess ta Cambridge Catherine ta haifi da namiji, a cewar fadar Kensington.

An dai dauke ta ne a mota daga fada zuwa asibitin St. Mary dake Paddington a yammacin London, tare da mijinta Duke na Cambridge da sanyin safiya.

Wannan jariri shi ne na uku a jerin wadanda ke jiron gadon sarautar Burtaniya.

Manema labarai na duniya sun kafa sansani a wajen asibitin na St. Mary, inda suka kwashe kwanaki suna jiran labarin haihuwar.

Tawagar manyan likitoci ne ke kula da mai nakudar, inda tsohon mai kula da lafiyar sarauniya, Marcus Setchell ke jagorantarsu.