Fitsarin dan'Adam na cajin wayar salula

Wayoyin salula
Image caption Wayoyin salula

Masana kimiyya a karon farko sun yi nasarar cajin wayar salula da fitsarin bil'adama.

Gwajin da aka yi a jami'ar yammacin Ingila ya gano cewa lita daya na fitsari na samar da makamashin da za a iya kiran waya na tsawon mintoci shida da aika sakonni.

Suna fatan wannan bincike zai taimakawa al'umomin dake fama da matsalar wutar lantarki ko rashin wutar baki daya.

Google

Wani jami'in kungiyar Tarayyar Turai ya ce shafin matambayi ba ya bata na Google ya gaza kawar da damuwar da ake da ita cewa, ya fi ba da fifiko ga muradunsa yayin ba da amsar tambayoyi.

Google ya sha kokarin ba da shawarwarin da da za su kwantar da hankula, amma akwai bukatar ya kara kaimi fiye da hakan, a cewar jami'in mai kula da gogayya na kungiyar tarayyar Turan.

Google na fuskantar matsin lamba tun bayan da ya sabunta manhajar taswirarsa.

Duk da cewa ya kara sabbin abubuwa, Google ya cire tsibirin Jura dake Scotland a taswirorinsa, ya bar wani titi daya kacal a tsakiyar teku.

PayPal

Shafin PayPal ya amince cewa mai yiwuwa kaunar da ya nuna ga wani kwastomansa ta wuce kima, bayan a bisa kuskure ya tura masa dalar Amurka malala.

Mutumin da ya tsinci dami a kala, Chris Reynolds, ya gano kudin ne a lokacin da ya ke duba bayanin asusun bankinsa na wata-wata, inda ya ce abin da ban al'ajabi.

Sai dai murnarsa ta koma ciki bayan PayPal ya kwashe kudinsa ya bar asusun Chris ba ko kwandala.