Kungiyar Hezbollah ta nuna bacin ranta

Dakarun Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon
Image caption Dakarun Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon

Kungiyar Hezbollah ta ba da sanarwa mai cike da bacin rai da ke nuna rashin amincewar ta da shawarar da Tarayyar Turai EU ta yanke a kanta.

Kungiyar ta EU dai ta saka bangaren kungiyar ta Hezbollah na soji a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kungiyar ta Hezbollah ta Lebanon, ta bayyana matakin a matsayin wani abu na nuna kiyayya kuma abinda bai dace ba.

Ta ce turawan sun yi aiki ne kawai da matsin lamba daga Amurka da Isra'ila.

Tun farko wani mai magana da yawun gwamnatin Amurka ya ce, matakin da Tarayyar Turai ta dauka na haramta aike wa kungiyar Hezbollah kudade daga Turai din, sako ne ga kungiyar dake Lebanon cewa babu yadda za a yi ta rinka gudanar da harkokin ta, ba tare da la'akari da sakamakon da za su haifar ba.