An sallami Kate da jaririnta daga asibitin London

Yerima William da Gimbiya Kate da jaririnsu
Image caption Yerima William da Gimbiya Kate da jaririnsu

Yau Talata da maraice ne aka sallami Duchess of Cambridge, uwargidan Yerima William, daga asibiti tare da dan da ta haifa masa.

Tun farko, Kate da Yerima William sun fito rike da jaririn, inda suka nuna shi ga manema labarai da sauran jama'ar da suka yi dafifi a kofar asibitin na St Mary's dake London.

Kafin daga bisani su dauke shi a mota su nufi gida, wato fadar Kensington.

Wannan jariri shi ne na uku a jerin masu jiran sarautar Birtaniya.

Yarima William ya ce shi da matarsa Duchess ta Cambridge ba za su iya kwatanta farin cikinsu game da samun karuwar dan su na fari ba.

Mahukuntan fadar Buckingham sun ce an haifi jaririn ne da misalin karfe hudu da minti 24 na yammacin jiya, kana yana da nauyin kilo uku da rabi.

Sarauniya da Mijinta Duke na Edinburg na cikin farin cikin samun wannan labari, yayinda Yarima William ya shafe daren jiya a asibiti tare da matarsa mai jegon da jaririnsu.

Jaririn wanda za a yiwa lakabi da Yariman Cambridge, shi ne na uku a jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya, zai kuma zama shugaban sauarn kasashe renon ingila 15.

Ana ci gaba da samun sakonnin taya murna daga sassa daban daban na duniya.