Amurka ta jinkirta bai wa Masar jiragen yaki

jirgin yaki sampurin F-16
Image caption jirgin yaki sampurin F-16

Shugaba Obama ya jinkirta gabatarwa Masar jiragen saman yaki samfurin F-16 ga hukumomin Masar, makonni uku bayan soja sun tumbuke gwamnatin Muhammad Morsi.

Kakakin ma'aikatar tsaro ta Pentagon, George Little ya ce, bai dace ba halin da kasar Masar take ciki yanzu a mika ma ta wadannan jiragen yaki.

Cikin watan Agusta dai ya kamata jiragen yakin su isa Masar.

Wakiliyar BBC ta ce ya dauki matakin dakatar da mikawa Masar din wadannan jiragen yaki hudu samfurin F-16 ne cikin daren jiya, bisa shawarar mashawartansa ta fuskar tsaro.