Me ya sa Musulmin Faransa ke tura gawa gida?

Wata tsohuwar makabarta a Morocco
Image caption Wata tsohuwar makabarta a Fes dake Morocco

Ana samun wata al'ada a tsakanin al'ummomin dake garuruwan da mazaunansu ma'aikata ne da kuma a biranen Faransa, ta maida gawawwaki zuwa kauyukan Algeria da Morocco.

A duk shekara a kan dauki dubban gawawwaki daga Faransa zuwa Maghreb, saboda iyalai Musulmai na tura gawawwakin 'yan uwansu kasashensu na asali domin binne su a can.

Al'amari ne dake bukatar kashe makudan kudade, domin tura gawa gida ya hada da batun jiragen sama, neman takardu daga ofisoshin jakadanci da kuma masu jana'iza na musamman.

Hakan yasa wasu ke ganin me yasa ba za a binne su a Faransa ba?

Tunda wadannan iyalai na zaune ne a Faransa, bai fi ba idan sun mutu kuma aka binne su a Faransar?

Amsar wannan tambaya dai ta ta'allaka ne da sarkakiyar dake tattare da zama dan kasa, a kasar dake da dumbin masu hijira.

Bugu da kari kuma Faransa na bin tsarin rarrabe mulki da addini, kana da kin yarda ta sauya matsayinta.

Jana'iza

A wani gidan jana'iza dake arewacin Faransa, a kan kira Abdallah Hadid kan a waya sau uku zuwa hudu a rana, daga iyalan da wani nasu ya rasu.

BBC ta yi hira da shi a lokacin da yakesintiri tsaknin ofisoshin jakadancin Algeria da Morroco, domin neman takardun izinin hukumominsu.

Yace "Zan iya cewa, kusan kashi 70 cikin 100 na iyalan wadanda aka yi wa rasuwa, sun fi son su tura gawar 'yan uwansu Algeria ko Morocco ko ma dai inda suka fito."

Yayin da ake yiwa gawar sutura kuma a sallace ta, tawagar gudanarwarmu za su garzaya domin nemo takardun da ake bukata daga dakin taro ko wajen 'yan sanda da kuma ofisoshin jakadanci."

Ya cigaba da cewa "Daga nan ne kuma za mu sayi tikitin jirgin sama ga iyalan, sannan mu biya kudin akwatin gawa wanda ake ajiye shi a wajen ajiye kaya na jirgi."

Image caption Abdallah Hadid, wani musulmi mai gidan jana'iza a Faransa

"Mutane ba su san abin da ke faruwa ba, domin yawancin jiragen sama dake tashi daga Faransa zuwa manyan biranen arewacin Afrika na dauke da akwatin gawa daya zuwa hudu, ya danganta da girman jirgin."

"Wani lokaci daga can kauye a gida ne ake tattara kudin da za a biya wajen maida gawar gida. Kuma a kan kashe kusan kudin euro 2,500 wato daidai da fam 2,150."

Abdallah ya bayyana cewa "Sai dai a halin yanzu mutane da dama na amfani da kamfanonin inshora, suna biyan kudi kalilan a duk shekara, domin tabbatar da cewa idan sun mutu za a samu isasshen kudin da za a maida gawarsu kasar haihuwarsu."

Dalilai

A cewar Abdallah akwai manyan dalilai biyu dake sa 'yan uwan mamaci, ke mayar da gawar dan uwansu Maghreb.

Na farko shi ne, saboda kauna da tunawa da kasarsu da kuma kishin kasar ta su.

Na biyu kuma, saboda babu makabartar musulmai a Faransa.

Faransa na kiran kanta kasar dake rarrabe harkokin siyasa da addini, kuma ta kwashe shekaru 100 tana hakan.

Hakan na nufin, idan aka zo batun makabartu, majalisun garuruwa dake bada filayen makabartun, ba sa duba batun addini.

Shekaru da dama, musulmai a Faransa sun yi ta kokarin ganin an basu makabartu a cikin garin, saboda a cikin makabartun za su iya kwantar da mamaci, fuskarsa na kallon al'kibla kamar yadda musulunci ya tanada.

Sai dai kuma Faransa ta nuna halin ko in kula.

Image caption Wata makabarta a Faransa

Makabarta

A zahiri ana kebe inda ake binne musulmai a makabartun hadakan, saboda musulmai na binne gawawwakin junansu kusa da kusa.

Ko da yake an barsu su yi hakan, amma ba a hukumance ba, domin babu wata manufa ta gwamnati data amince da hakan.

Wata matsalar da musulmai ke fuskanta a makabartun Faransa ita ce, ana kayyade shekarun da gawa za tayi a cikinsu.

Iyalai na karbar hayan guri na tsawon shekaru 30 zuwa 50, inda bayan nan sai su maida gawar cikin wani babban kabari.

Hakan dai ya sabawa musulmi da dama, wadanda suka yi imanin cewa ba a tono mamacin da aka binne.

Kuma ba sa so su dora nauyin sake karbar hayar filin da kabarin yake ga al'ummarsu masu tasowa.

Saboda haka sun gwammace su tura gawa gida, kodayake akwai wasu dake da ra'ayin binne mamatansu a Faransar.

Akwai dai Musulmi kimanin miliyan shida a Faransa.