Majalisa ta cire kariya ga shugaban kasa

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta kada kuri'ar amince wa da tube wa shugaban kasa da kuma gwamnonin kasar rigar kariya.

Haka kuma ta amince da soke hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohi.

Majalisar ta cimma hakan ne a daren ranar Laraba lokacin da take duba rahoton kwamitinta kan gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Majalisar wakilan ta kuma amince da cin gashin kan kananan hukumomi.

Wasu daga cikin abubuwan da majalisar ta amince da su, kamar tube rigar kariya ga shugaban kasa da gwamnoni da kuma cin gashin kan kananan hukumomi, sun sha bamban da matakin da majalisar dattawan kasar ta dauka a kansu.

Da fari dai majalisar ta dakatar da kada kuri'ar, saboda matsalar da aka samu da injinan kada kuri'ar.