Mutane fiye da 70 sun mutu a Spain

Image caption Mutane da dama sun mutu a hadarin jirgin Spain

Mutane 77 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin jirgin kasa a kasar Spain, yayin da wasu fiye da dari suka jikkata.

Jirgiin wanda ke gudu ya goce ne daga kan layin dogo a arewa maso yammacin Spain.

Jirgin na tafiya ne kan hanyarsa ta zuwa Ferrol daga Madrid, a lokacin da lamarin ya auku.

Gwamnatin yankin dai ta yi rokon gaggawa kan bada jini domin wadanda suka samu raunuka.

Jirgin kasar dai wanda ke zirga-zirgarsa tsakanin birane a kasar na dauke da fasinjoji sama da 200.

Hotunan da aka dauka jim kadan bayan hadarin, ya nuna gawawwaki da aka rufe da bargo.

Karin bayani