'Artabu ba zai magance yakin Syria ba'

Image caption Amfani da karfin soji ba zai kawo karshen yakin Syria ba

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da kuma na Kungiyar Kasashen Larabawa na musamman ga Syria, Lakdar Brahimi, yace ba za a iya shawo kan yakin basasar Syria ta hanyar amfani da karfin soji ba.

Mr Brahimi yayi gargadin cewar kaiwa 'yan tawayen Syria ko kuma gwamnatin Bashar Al Asad makamai, zai kara tsawaita rikicin ne kawai , ba tare da kawo karshen sa ba.

Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya, na ganin tura makamai ba shine mafita ba.

A cewar Brahimi, dole ne a dakatar da tura makamai, a koma hanya ta siyasa domin warware rikicin.

Karin bayani