An kammala share gubar dalma a Zamfara

Ayyukan hakar ma'adanai
Image caption Ayyukan hakar ma'adanai

Gwamnatin Najeriya da kungiyar likitoci masu bada agaji ta duniya, MSF sun ce an kammala share gubar dalma tare da sauya kasa, a kauyukan da suka gurbace a jahar Zamfara.

An dai kammala aikin ne da kauye Bagega wanda shi ne wuri mafi girma da ya fi gurbata.

Kungiyoyin agajin sun bayyana aikin da cewa wani aiki da ba a saba gani ba, wanda ya ceto rayukkan yara da dama daga salwanta.

Abin da ya rage yanzu a cewarsu shi ne ma'aikatar lafiya da ta ma'adinai na kasa, su shiga yankin domin yiwa sauran yaran magani da kuma tabbatar da ana hakar ma'adinai bisa ka'ida.

A shekarar 2011 gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar samun wasu kauyukan da ake hakar ma'adinai a asirce, wadanda kasar su ta gurbata, kuma har yanzu ba a gano su ba.

Sai dai ma'aikatar Muhalli ta kasa tace har yanzu ba a gano wasu sabbin wuraren da ake hakar ma'adinan ba.

Daruruwan yara ne suka mutu sakamakon shakar gubar dalmar tun daga shekara ta 2010.

Hukumar lafiya ta duniya WHO da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, sun bayyana lamarin a matsayin matsalar gubar dalma mafi muni a tarihi.