Al'ummar Bama sun koka game da kuncin rayuwa

Image caption Dakarun soji a Maiduguri

Wasu rahotanni dake fitowa daga garin Bama na Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana irin kuncin rayuwar da jama'ar garin ke kukan suna fuskanta a karkashin dokar ta-bacin da aka kafa.

Al'ummar yankin sun zargi jami'an tsaro da hanasu shiga da fita, da kuma yadda suka ce ana kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a yakin da sojojin Najeriya ke yi da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ne ya kafa dokar ta baci a jihar Borno da Yobe da kuma Adamawa a yinkurin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Tun lokacin da aka kafa dokar ta ba ci ake zargin jami'an tsaro da wuce gona da iri suna azabtar da fararen hula, zargin da dakarun suka musanta.

Karin bayani